Asabar, Fabrairu 28, 2015 Karfe 07:52

Najeriya

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Kan Kwambar Ado Bayero

Jami'ai suka ce mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, bai ji rauni ba a lokacin da aka kai farmaki a kan kwambar motocinsa asabar din nan.

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado BayeroMai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero
x
Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero
Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero
Wasu 'yan bindiga a Najeriya sun kai farmaki a kan kwambar motocin daya daga cikin manyan shugabannin Musulmi na kasar, suka kashe mutane uku.

Jami'ai suka ce mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, bai ji rauni ba a lokacin da aka kai farmaki a kan  kwambar motocin nasa asabar din nan.

Ya zuwa yanzu, babu wanda ya dauki alhakin kai wannan hari a birnin Kano, birni mafi girma a yankin arewacin Najeriya.

Wannan lamari ya faru ana saura kwana daya tak a cikia shekara guda da mummunan harin bama-bamai da harbe-harben da ya kashe mutane 184 a birnin na Kano. An dora laifin harin na bara a kan kungiyar nan ta Boko Haram.

Kungiyar ta Boko Haram tana ikirarin cewa tana gwagwarmayar bkafa dokokin Shari'a ne a fadin Najeriya, kasar da akasarin mutanen arewacinta Musulmi ne, yayin da Kirista suka fi rinjaye a kudu.
An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: Aliyu Jibia Daga: Jibia katsina
28.01.2013 20:07
Asalamu alaikum, sashen hausa na muryar amuruka. Ina san inbai yanna ra.ayina akan abinda ke faruwa akasar masar, yakamata mutannan kasar masar sugode ma Allah akan baiwar da Allah ya masu sudaina yawan zangazanga da tada tarzoma

Audio Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi :      0700 - 0730 UTC

Audio Shirin Rana :        1500 - 1530 UTC

Audio Shirin Dare :         2030 - 2100 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12026190548 ko kuma +12026190551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Sauti