Asabar, Fabrairu 28, 2015 Karfe 02:56

Najeriya

Najeria Ta Ci Kofin Kwallon Kafar Nahiyar Afirka Na 2013

Kungiyar kwallon kafar Najaria ta lashe kofin gasar kwallon kafa na nahiyar Afirka na shekarar 2013 a Afirka ta Kudu, nasara akan Burkina Faso da ci 1-0.

Mai tsaron raga Victor Enyeama.Mai tsaron raga Victor Enyeama.
x
Mai tsaron raga Victor Enyeama.
Mai tsaron raga Victor Enyeama.
WASHINGTON, D.C -- A karo na farko da kungiyar Super Eagles din ta ci wannan wasa tun shekara ta 1994 a Tunisiya, Najeria ta zama kasa ta hudu a duk fadin Afirka da ta ci wannan kofi sau uku ko sama da haka.
 
Dan wasa Sunday Mba na kungiyar Warri Wolf ne ne ya fara jefa kwallo minti 40 da saka wasa.
 
Jagoran kungiyar, Coach Stephen Keshi ya shiga cikin littatafan tarihi a matsayin mutum na biyu wanda yaci kofin a matsayin dan wasa, da kuma jagora.
 
Bayan samun nasara akan kungiyoyin Ivory Coast da Mali, magoya bayan Najeria sun nuna karfin gwiwar samun nasara a wasan na karshe. 
 
Dan gaba Emmanuel Emenike ne ya karbi kyautar wanda yafi kowa jefa kwallaye a raga da guda hudu a gasar baki daya.
 
Magoya bayan kungiyar Super Eagles na murna a fadin duniya, duk da halin da kasar take ciki a yanzu, kamar rashin tsaro, kashe-kashen jama'a, fashe-fashen bom, rashin ayyukanyi da karancin kayan more rayuwa.

Rabon Najeria da buga wasan karshe a wannan gasa tun shekara ta 2000 a inda kasar Cameroon tayi nasara a bugun fenariti da ci 4 da 3. Sau biyu Najeria tana cin kofin a wasan karshe, a shekara ta 1980 a gida Najeria, da kuma 1994.
 
A cikin jami'an da suka gabatar da kofin, harda shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Sepp Blatter, Shugaban Kasar Afirka ta Kudu Zacob Zuma, da Isa Hayatou shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka.

Audio Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi :      0700 - 0730 UTC

Audio Shirin Rana :        1500 - 1530 UTC

Audio Shirin Dare :         2030 - 2100 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12026190548 ko kuma +12026190551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Sauti