Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abunda Akayi Wa ‘Yan Majalisa Yayi – inji Wasu


Wasu magoya bayan kakakin majalisar wakilai Aminu Waziri Tambuwal, suka kutsa da shi cikin majalisa duk da yunkurin ‘yan majalisa na hana shi shiga.
Wasu magoya bayan kakakin majalisar wakilai Aminu Waziri Tambuwal, suka kutsa da shi cikin majalisa duk da yunkurin ‘yan majalisa na hana shi shiga.

Biyo bayan abunda ya faru a majalisar wakilan Najeriya Alhamis dinnan, jama’ar kasar na cigaba da bayyana ra’ayoyinsu, game da abunda ya faru.

A kudu maso yammacin Najeriya, jama’a sun bayyana mamakinsu ga irin rawar da jami’an tsaro suka taka a wajen wannan badakala.

Jama’ar Jihar Oyo sun nemi shugaba Goodluck Jonathan yayi gaggawar sauka daga karagar mulki.

Mallam Umaru Ja’e, cewa yayi “gaskiya abunda anka aikata baiyi daidai ba, masu bada doka da kansu, a ce suma an hana su zama.”

Shi kuwa Alhaji Issuhu Abubakar cewa yayi “wannan abun kunya ne a duk duniya, ba ma a Najeriya kadai ba, saboda haka, yanzu gwamnatin Najeriya, shi Jonathan ya kamata ya sauka. Wannan abun kunya, duk duniya.”

Amma ga Mallam Kyari Ali Bukar, harbawa ‘yan majalisar barkonon tsohuwa, da rufe kofofin majalisar abun nazari ne ga shuwagabanni a Najeriya.

“Gaskiya fisa billiLahi abunda ‘yan sanda suka yi, ba dai-dai bane, ba shine doka ba, amma kuma yayi haka, da akayi musu. Saboda su ‘yan majalisa da kansu, akwai matsala a tare da su. Ana kashe mutane, suna ji kullum, kuma sune doka, sun san da wannan abun. Aka kyale, har gashi ya kai ya kawo ana saka borkono a idanunsu.”

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:13 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG