Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CBN Ya Fitar Da Jerin Sunayen Bankunan Ajiya Masu Lasisi


Babban bankin Najeriya CBN
Babban bankin Najeriya CBN

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar da sunayen bankunan ajiya masu lasisi dake gudanar da harkokinsu a kasar.

Domin kara fayyace yadda harkar banki take a Najeriya, Babban Bankin Najeriyar ya wallafa jerin sunayen bankunan ne a shafinsa na yanar gizo a jiya Talata.

Bankunan dake da sahalewar gudanar da hada-hadar kasa da kasa sun hadar da Access da Fidelity da Fcmb da First Bank da Guaranty Trust da Uba da kuma bankin Zenith.

Su kuwa bankunan kasuwancin dake da sahalewar gudanar da harkokinsu a iya cikin Najeriya sun hadar da Citibank da Ecobank da Heritage da Globus Bank da kuma Keystone; sauran sun hadar da Polaris da Stanbic Ibtc da Standard Chartered da Sterling da Titan Trust da bankin Union da Unity da Wema da Premium Trust da kuma Optimus Bank.

Bankunan kasuwancin dake da lasisin gudanar da harkokinsu a iya wani yanki sun hadar da Providus da Parallex da Suntrust da kuma Signature bank.

Su kuwa bankunan da ba ruwansu da kudin ruwa dake da sahalewar gudanar da hada-hadarsu a Najeriya sun hada da Jaiz da Taj da Lotus da kuma Alternative Bank.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG