Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EFCC Na Da Hurumin Tilastawa Ma'aikatan Banki Su Bayyana Kadarorinsu - Falana


Babban lauya mai mukamin SAN, Femi Falana
Babban lauya mai mukamin SAN, Femi Falana

Fitaccen lauya mai mukamin SAN, Femi Falana, ya ce, hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa na da hurumin tilastawa manyan ma’aikatan banki bayyana kadarorin da suka mallaka.

Lauyan ya kara da cewa nauyin da ya rataya a wuyanta na tabbatar da cewa, ta aiwatar da tanadin dukannin dokokin da ke da nasaba da laifuffukan cin hanci da rashawa saboda haka, dokar Najeriya ta ba wa EFCC ikon gudanar da bincike kan kadarorin kowane mutum kamar yadda sashi na 7 sakin sashi na 1(b) na dokar hukumar na shekarar 2004 ya bayyana.

Har ila yau, kungiyar Transparency International, mai yaki da cin hanci da rashawa ta kasa da kasa ta jaddada cewa, idan har aka aiwatar da tanadin dokar ma'aikatan banki na bayyana kadara na shekarar 1986 yadda ya kamata, a kowacce shekara, Najeriya na iya adana dala biliyan 15 zuwa 18 na haramtattun kudadde da ake fitarwa ya hanyoyin da bai kamata ba.

Falana dai ya yi wannan karin haske kan nauyin da ya rataya a wuyan hukumar EFCC yayin amsa tambayoyin manema labarai kan hurumin EFCC na tilastawa ma’aikatan banki su bayyana kadarorin da suka mallaka a karkashin doka.

Idan ba a manta ba a cikin wannan makon ne shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya ba wa ma’aikatan banki umarnin su bayyana kadarorin da suka mallaka daga watan Maris zuwa Yuni.

Dokar dai, ta ce a cikin kwanaki 14 da fara aiki duk ma’aikacin banki ya bayyana kadarorin da ya mallaka inda sashi na 7 sakin sashi na 1 ya ce babban laifi ne a samu ma’aikacin banki da kadarorin da suka zarta kudadden shigarsa kamar yadda za a iya tantancewa.

XS
SM
MD
LG