Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kirsimeti: Musulmai A Jos Sun Ziyarci Kirista A Majami'ar ECWA


Wassu Musulmi da ga kungiyar Islamic Movement of Nigeria sun ziyarci masujadar ECWA Seminary a Jos don tayasu bikin Kirsimeti.
Wassu Musulmi da ga kungiyar Islamic Movement of Nigeria sun ziyarci masujadar ECWA Seminary a Jos don tayasu bikin Kirsimeti.

Mabiya addinin na Kirista da Musulmi sun jaddada muhimmancin hadin kai da daina nuna wa addinan juna kyama da tsangwama don samun ci gaba da wanzarda zaman lafiya.

Wasu Musulmai daga kungiyar Islamic Movement of Nigeria sun ziyarci masujadar ECWA Seminary a Jos don taya su bikin zagayowar ranar haihuwar Yesu Almasihu wadda mabiya addinin Kirista ke yi a ranar 25 ga watan Disamba a kowani shekara.

Mabiya addinin na Kirista da Musulmi sun jaddada muhimmancin hadin kai da daina nuna wa addinan juna kyama da tsangwama don samun ci gaba da wanzarda zaman lafiya.

Limamin majami'ar ECWA Seminary da ke Jos, Ravaran Solomon Guruza yace ziyarar da al'ummar Musulmin suka kawo cocin zai karfafa dankon zumunci da fahintar juna.

Jagorar kungiyar musulmin, Nura Waziri yace shugabansu ya dora su a kan akidar hadin kai ne ba rarrabuwa ba.

Shima Yakubu Ibrahim, wadda ya ke cikin tawagar, yace rashin fahintar juna ya kasance babbar matsala, don haka yake ganin irin wannan ziyara zai taimaka wajen warware matsalar.

Malama Zakiyya Abubakar tace suna bukatar a dinke barakar dake tsakanin addinai.

Bikin na Kirsimeti zai cigaba da ziyarar yan'uwa da abokai da bada kyaututtuka.

A wani labari na daban kuma, gwamman mutane ne rahotanni ke cewa 'yan bindiga sun hallaka su a wassu hare-hare cikin dare, da ake zaton an shirya ne kan kauyuka da dama a kananan hukumomin Bokkos, Barkin Ladi da Mangu.

Bayan kashe-kashen an kuma kone rumbunan abinci, gidaje, motoci, rugage da sauran dukiyoyi.

Tuni dai gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya umurci jami'an tsaro su nemo wadanda suka aikata danyen aiki.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG