Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Tsaro Na MDD Ya Amince Da Kudurin Samar Da Kudaden Ayyukan Samar Da Zaman Lafiya A Afirka


Shugaban kasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, yayin da yake jawabi a zauran Majalisar Dinkin Duniya
Shugaban kasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, yayin da yake jawabi a zauran Majalisar Dinkin Duniya

Al-Hassan Bello, mai sharhi kan harkokin kasa da kasa da tsaro, ya ce amincewa da kudurin wata nasara ce ga yaki da ta’addanci a nahiyar.

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kudurin Afirka a hukumance, wanda Ghana ta jagoranta da hadin gwiwar kasashen Gabon da Mozambique, da ke neman wajibcin bayar da tallafi da kuma ba da kudaden gudanar da ayyukan zaman lafiya da tunkarar duk wata barazana ga zaman lafiya da tsaro a kasashen Afirka, fiye da wadanda majalisar ta saba gudanarwa.

Hakan ya bayyana ne a wata sanarwa da Ma’aikatar Hulda da Kasashen Waje da Hadin Kan Yanki na Ghana ta fitar ga manema labarai.

Sanarwar ta ce, a matsayinsa na shugaban majalisar na watan Nuwamba, 2022, shugaban kasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo da Ministar Harkokin Waje, Shirley Ayorkor Botchwey, sun gudanar da muhawara kan batutuwan da suka shafi karuwar barazanar tsattsaurar ra’ayi da ta'addanci a Nahiyar Afirka.

Sun ba da misalin yankin Sahel da gabar tekun Yammacin Afirka, tare da yin kira da a samar da kudaden gudanar da ayyukan kariya da Afirka ke jagoranta ta hanyar gudummawar da Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar.

Zauran Kwamitin Sulhu Na Majalisar Dinkin Duniya
Zauran Kwamitin Sulhu Na Majalisar Dinkin Duniya

Al-Hassan Bello, mai sharhi kan harkokin kasa da kasa da tsaro, ya ce amincewa da kudurin wata nasara ce ga yaki da ta’addanci.

Ya ce “Nasara ce ga yaki da ta’addanci da muke samu a Afirka ta Yamma. Na biyu, kwamitin tsaro kuma ya fahimta cewa rashin tsaro ya canja daga yadda yake a baya. Na uku, kwamitin tsaro da kan sa ya fahimci cewa, hanyar da ka bi na farko kan tsaro ba a samu sakamakon da ake bukata ba; kamar yadda aka yi a Mali, inda kasashe kamar Faransa, da Jamus duka aika dakaru don neman zamn lafiya. Mafi cancanta ne masu matsalar su magance matsalarsu da kan su; mu Afirka mu kokarta mu kiyaye ta’addanci”.

A karkashin wannan kudurin, dukkan ayyukan zaman lafiya da ke karkashin jagorancin kungiyar Tarayyar Afirka, AU da kwamitin tsaro na MDD ya amince da su, za su samu tallafin MDD da aka tantance, na gudunmawar da ya kai kashi 75 cikin 100 na kasafin kudi na shekara-shekara da. Sai sauran kudaden kuma, hadin gwuiwar Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Tarayyar Afirka ne za su tattaro daga kasashen duniya. Majalisar ta kuma yi alkawarin yin la'akari da duk hanyoyi mafi dacewa a yayin da aka samu gibi wajen tattara kudade.

Ministar Harkokin Wajer Gahna, Shirley Ayorkor Botchwey, yayin da take jawabi a zauran MDD
Ministar Harkokin Wajer Gahna, Shirley Ayorkor Botchwey, yayin da take jawabi a zauran MDD

Da take tsokaci game da amincewa da kudurin, ministar harkokin waje, Madam Shirley Ayorkor Botchwey ta ce, “Yau babbar rana ce ga Afirka da diflomasiyya.

AbdulMajid Musa, mai shiga tsakani, kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum ya ce, alheri ne ga Afirka domin cikas da ake samu wurin kawo zaman lafiya shi ne lamarin kudi; yadda za a samu kudaden biyan sojoji da kayan yaki. Yanzu da yake MDD za ta taimaka, ba za’a samu cikas ba, domin za ta taimaka da batun kudi. Kuma wannan ci gaba ne ga Ghana, domin it ace ta fito da kudurin.

A wata sanarwa da jakadiyar Amurka a MDD Ambasada Linda Thomas-Greenfield ta fitar ga manema labarai ta ce, “Amurka na nuna godiyarta ga Ghana, bisa jagorancinta da hadin gwiwa ga wannan tsarin, da kuma dukkan mambobin kwamitin tsaro na Afirka guda uku. Muna dokin tabbatar da burinta ta hanyar yin aiki tare da AU kan tura tawagar inganta zaman lafiya da kare fararen hula a Nahiyar da ke fuskantar barazanar tsaro.”

Idris Abdallah Bako:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG