Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Tararrayyar Najeriya Na Nazarin Gayyatar Shugaban Kasa Da Gwamnoni


Taron Yan Majalisa Da Sanatoci Da Aka Yi A Hade
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:05 0:00

Taron Yan Majalisa Da Sanatoci Da Aka Yi A Hade

Majalisar Wakilai ta kawo wani kudurin da zai ba Majalisar karfin ikon gayyatar Shugaban Kasa da Gwamnonin Jihohi zuwa gabanta domin su amsa tambayoyi akan gudanarwa idan bukatan haka ta taso.

Wannan kudurin doka da wani dan Majalisar mai wakiltan yankin jihar Edo, Sergius Ogun ya gabatar, tuni har an riga an yi masa karatu na biyu a zauren Majalisar wakilai, kuma idan wanan kuduri ya samu shiga, Majalisa za ta iya tursasa Shugaban kasa da gwamnoni su bayyana a gaban ta domin amsa tambayoyin da aka bijiro masu a duk lokacinda bukatar haka ya taso.

Karin bayani akan: Majalisar Dattawa, Abdullahi Balarabe Salame, jihar Edo, Shugaba Muhammadu Buhari​, Nigeria, da Najeriya.

Dan Majalisar Wakilai daga Jihar Sokoto Dokta Abdullahi Balarabe Salame ya ce wannan doka dama babu ita a cikin kundin tsarin mulki da ta yi bayani karara cewa ana iya kiran Shugaban kasa zuwa gaban Majalisa, amma akwai abinda ake kira resolution a turanci. Saivdai Dokta Salame ya ce dokar ba ta da wani alfanu ko da an yi dokar saboda tana iya kawo yamutsi a harkar gudanarwa saboda kundin tsarin mulki ya rarraba wa ko wanne sashi aikin da ya kamata ya yi. Abdullahi Balarabe Salame ya ce akwai muhimmin aiki da aka ware wa bangaren Majalisa baya ga yin doka, shi ne sa ido a bangaren zantarwa, saboda haka wannan doka ba za ta yi wani amfani ba.

Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

A lokacin da yake nashi nazari Sanata Mai wakiltan Nasarawa ta yamma Abdullahi Adamu ya ce wannan kudurin doka bai riga ya isa Majalisar Dattawa ba tukuna. Sanata Abdullahi Adamu ya ce abu ne mai wuya ne irin wannan kudurin ya samu karbuwa a Majalisar Dattawa domin daga dukan alamu akwai wani nufi da wadanda suka kawo kudurin suke da shi, kuma ba nufi ne mai kyau ba tunda kundin tsarin mulki ya rabawa kowane bangare aikin sa. Wani bangare ba zai shiga na wani ba,saboda a samu ci gaba mai dorewa.

Amma tsohon dan majalisar Dattawa daga Jihar Kaduna ta tsakiya Komred Shehu Sani yana ganin yin irin wannan doka ba laifi ba ne domin zai ba Majalisa dama ta yi aikin ta yadda ya kamata, kuma kasa za ta fi samun amfani idan har ana amfani da dokokin yadda aka tsara su, ba tareda nuna fifiko ko son rai ba.

gwamnan-babban-bankin-najeriya-zai-bayyana-gaban-majalisa-don-yin-bayani-kan-cryptocurrency

sarakunan-gargajiya-sun-kai-koke-majalisar-dattawa

majalisar-dattawa-ta-bukaci-buhari-ya-kafa-dokar-ta-baci-a-fannin-ilimi

Kokarin gyara dokar da yan Majalisar ke yi ya samo asali ne tun daga lokacin da Majalisar Wakilai ta nemi bayyanar Shugaban kasa a zauren ta amma kuma Ministan Shari'a Abubakar Malami ya gabatar da jinkiri da ya hana yin hakan.

Saurari rahoton Medina Dauda cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG