Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarakunan Gargajiya Sun Kai Koke Majalisar Dattawa


Sarakunan gargajiya.

Sarakunan kasa sun mika kokensu ga kwamitin Majalisar Dattawa da zai yi wa kundin tsarin kasar garambawul a karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo Agege, inda suka nemi a mayar masu da ikon da tsarin mulki ya basu a baya.

Shugaban Majalisar Sarakuna na Jihar Neja kuma Etsu Nupe Alhaji Yahaya Abubakar ne ya gabatar da bukatun sarakunan, inda suka nemi a mayar masu da ikon da kundin tsarin kasa ya ba su wanda aka yi watsi da shi ta hanyar dokokin sake fasalin kananan hukumomi a shekarun 1967 da 1976.

Etsu Nupe ya ce a tsakanin shekarun 1920 zuwa 1960, Sarakunan gargajiya suna da matukar tasiri kuma su ne masu kula da bukatun kananan hukumomi, saboda haka sun san dukkan wadanda ke shiga da fita a unguwanni a kasar.

Karin bayani akan: Sarakunan gargajiya, Majalisar Dattawa, Nigeria, da Najeriya.

Daya daga cikin ‘yayan kwamitin kuma Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa Tanko Almakura, ya bayyana muhimmacin irin rawar da Sarakuna suka rinka takawa wajen hadin kan kasa, wanda ya ke ganin cewa idan aka sake mayar masu da ikon da suke nema, Sarakunan za su taimaka wajen rage yawan matsalolin da ake fuskanta a fanin tsaro a kasar.

Shi ma Sanata mai wakiltar Taraba ta tsakiya, Yusuf Abubakar Yusuf, ya ce Majalisa za ta duba yiwuwar mayar wa Sarakuna da ikonsu domin su ne shugabannin kasa, masu fada a ji. Kuma su ne za su iya tafiyar da harkokin al'adu a kasar baki daya.

Amma shugaban rundunar adalci, Abdulkarim Daiyyabu, ya na gani wasu sarakunan suna yin abubuwan da basu dace ba.

Dokar bai daya ta Janar Aguyi Ironsi ta shekarar 1966, da kuma ta Janar Yakubu Gowon ta 1967, da Janar Olusegun Obasanjo ta 1976 kan kwaskwarimar kananan hukumomi bi-da-bi ne suka kwace wa sarakuna ikonsu tare da mika ikon ga kananan hukumomi.

Saurari rahoton Medina Dauda Daga.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00


Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG