Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Sufurin Jiragen Sama A Najeriya Sun Ja Daga


Tashar jirgin sama ta Murtala Muhammed agos, Nigeria.
Tashar jirgin sama ta Murtala Muhammed agos, Nigeria.

Masu harkokin zirga zirgar jiragen sama a Najeriya sun ja daga da hukumomi da cewa, ba zasu sake biyan kudin haraji ba saboda albazaranci da kungiyar tace ana yi a ma’aikatar harkokin sufurin jiragen sama

Masu harkokin zirga zirgar jiragen sama a Najeriya sun ja daga da hukumomi da cewa, ba zasu sake biyan kudin haraji ba saboda albazaranci da kungiyar tace ana yi a ma’aikatar harkokin sufurin jiragen sama.

A cikin hirarsu da wakilin Sashen Hausa Ladan Ibrahim Ayawa, kakakin kungiyar Alhaji Mohammed Tukur yace ba batun sayen motocin sulke da ma’aikatar tayi kadai ne ya tada masu da hankali ba, amma da batun kara yawan haraji da kuma wadansu albazaranci da ake yi a ma’aikatar ba tare da an yi wani abin azo a gani na inganta harkokin sufufin jiragen sama a kasar ba. Alhaji Tukur yace banda kwaskwarima da ake yiwa wadansu tashoshin jiragen saman kasar, babu wani abinda ake yi na inganta ayyukan sufurin jiragen sama kamar sauka da tashin jiragen.

Sai dai da yake maida martani, kakakin harkokin sufurin jiragen saman na Najeriya Yakubu Datti yace babu kanshin gaskiya a zargin na Alhaji Mohammed Tukur wanda ya bayyana a matsayin dan karen farautar masu sufurin jiragen saman. Ya kuma musanta cewa ana kara masu ba gaira ba dalili.

Ga cikakken rahoton
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00
Shiga Kai Tsaye
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG