Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsayar Shugaban Kwamitin Tattara Bayanan Sirri Na Majilisar Wakilan Amurka Kan Zaben 2016


Shugaban kwamitin tattara bayanan sirri na majilisar Wakilan Amurka, Davin Nunes, ya fada jiya litini cewa baya da niyyar tsame kansa ko kuma kin yin adalci akan aikin binciken da kwamitinsa keyi game da ko kasar Rasha tayi kutse a zaben shugaban kasar Amurka na shekarar data gabata.

Yace kome dai siyasa ce, mutane suna da yancin fadin abinda suke so su fada, wannan yayi dai-dai. Nunes yana Magana sa’ilin da yake wa manema labarai jawabi bayan da takwaran sa na jamiyyar Democrat, Adam Schiff, ya bada sanarwar cewa yana kira da Nunes, ya sauka daga shugabancin wannan kwamitin binciken.

A cikin sanarwar da Schiff, ya bayar yana cewa ne, “wannan bukatar da ta nemi shugaban kwamitin binciken wannan batu ya sauka ba Magana ce da nake dauka ‘yar karama ba, domin kuwa ni da shugaban wannan kwamitin munyi aiki na shekaru da dama tare,” yaci gaba da cewa zai yi wahala jama’a su amince da aikin wannan kwamitin binciken muddin ma ace ansa son rai cikin aikin, ko kuma yin yadda shugaban yaga dama.

Sai dai mai Magana da yawun Nunes, Jack Langer yace Nunes ya samu bayanan sa ne a fadar White House, kafin a satin daya shige ya fito fili ya bayyana cewa kaddara ce ta rutsa da Shugaba Donald Trump, game da nadar bayanan sa.

Langer, ya fada wa manema labarai jiya litini cewa Nunes, yana son ya samu wani kebabben wuri ne da zai bashi dammar nazarin wadannan bayanai da ya samu sabanin abinda ake hasashe. Da farko dai Nunes, bai bayyana inda ya samu bayanansa ba, kuma har yanzu din ma bai ce ga inda ya samo wadannan bayanan ba.

Sai dai shima dan majilisar wakilai daga jamiyyar Republican, Peter King, daga jihar New York, ya shaidawa muryar Amurka cewa Nunes, yayi abinda ya dace daga farko har karshe sai dai an tsaya kai da fata na ganin an tozarta shi da aikin da yake yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG