Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Sarkin Zazzau Na 19 Ya Yi Mubaya’a Ga Sarkin Musulmi


 Ziyayar Sarkin Zazzau na 19 Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli a Fadar Sarkin Musulmi
Ziyayar Sarkin Zazzau na 19 Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli a Fadar Sarkin Musulmi

Shugaban majalisar koli akan harkokin addinin musulunci a Najeriya, mai alfarma sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar ya bukaci wadanda suka nemi sarautar Zazzau basu samu ba, su hada kai da wanda aka zaba domin ciyar da masarautar gaba.

Mai alfarma ya furta hakan ne lokacin da ya karbi mubaya'ar sabon Sarkin Zazzau Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli a fadar sa.

Dangantaka tsakanin Cibiyar daular Usmaniya da masarautar Zazzau ta samo asali tun lokacin da Shehu Usmanu Danfodiyo ya baiwa Malam Musa tuta ta jaddada addinin musulunci a masarautar Zazzau.

Tun daga wannan lokacin duk wanda aka nada Khalifa a wannan masarautar sai yayi mubaya'a ga khalifan shehu Usman Danfodiyo domin jaddada wannan dangantakar.

an-nada-alhaji-ahmad-nuhu-bamalli-a-matsayin-sarkin-na-19-na-zazzau

gwamna-nasiru-el-rufai-na-jihar-kaduna-a-najeriya-ya-nada-magajin-garin-zazzau-alhaji-ahmad-nuhu-bamalli-a-matsayin-sarkin-na-19-zazzau

hira-da-mai-martaba-sarkin-zazzau-alhaji-ahmad-bamalli

Sarkin Zazzau na 19 Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli shima bai yar da gado ba domin ya je Sakkwato inda yayi mubaya'a ga sarkin musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar wanda shine Khalifan mujaddadi Danfodiyo. Ya baiwa khalifan tabbacin goyon baya da biyayya ga cibiyar ta daular Usmaniya. Ya kuma shedawa Sarkin musulmi cewa babu matsala a masarautar Zazzau kuma an tsayar da ranar 9 ga watan Nuwamba a zaman ranar da za a mika masa sandar girma.

Ziyarar Sarkin Zazzau na 19 Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli a fadar Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar
Ziyarar Sarkin Zazzau na 19 Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli a fadar Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar

Mai alfarma sarkin musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar ya nuna gamsuwa da wannan zumunci mai dadadden tarihi da Sabon sarkin ya jaddada ya kuma yi kira gareshi da yayi adalci ga kowa domin kowa nasa ne.

Wannan ziyarar da Sabon sarkin Zazzau na zuwa ne lokacin da daya daga cikin yan masarautar ta Zazzau Iyan Zazzau Bashir Aminu ya garzaya kotu yana kalubalantar nadin Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli a zaman sarkin na Zazzau.

Ziyarar Sarkin Zazzau na 19 Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli a fadar Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar
Ziyarar Sarkin Zazzau na 19 Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli a fadar Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar

Saurari rahoton Muhammadu Nasir cikin sauti;

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG