Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli Ya Zama Sarkin Zazzau Na 19


HRH Ahmed Nuhu Bamalli
HRH Ahmed Nuhu Bamalli

Bayan dan tsaikon da aka samu da kuma jita-jita kan ko waye zai zama sabon sarkin Zazzau, yanzu wannan ya zama tarihi saboda an nada Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau.

HRH Ahmed Nuhu Bamalli
HRH Ahmed Nuhu Bamalli


Gwamna Nasiru El-Rufai na jahar Kaduna ya nada Magajin Garin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sarkin na 19 Zazzau.

Biyan da Masarautar Zazzau ta aika wa wa Gwamna Nasiru El Rufai sunayen mutum uku daga cikin mutum 11 da suka nuna sha’awarsu ta maye gurbin Sarkin Zazzau marigayi, Alhaji Shehu Idris da ya rasu a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba bayan da ya kwashe shekara 45 akan karagar mulkin masaruatar.

Ya rasu yana da shekara 84.

An Haifi Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ne a ranar 8 ga Yuni, 1966 a Zariya, mahaifinsa, Nuhu Bamalli ne ya rike Magajin Garin Zazzau kafin a sauya masa sarautar.

Ga sanarwar nadin sabon sarkin, ta bakin Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautun Jahar Kaduna, Alhaji Jafaru Ibrahim Sani, kamar yadda wakilinmu, Isah Lawan Ikara ya aiko mana:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:54 0:00


Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG