Amurka za ta bayar da kusan dala miliyan 55 don magance matsalar jin-kai a Burkina Faso, in ji jami’ar bayar da agaji ta Amurka Samantha Power a ranar Alhamis, a cewar wata sanarwa da Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya gani.
Wata kungiyar 'yan tawaye da ake zargin tana da alaka da kasar Rwanda ta kwace garin Rubaya da ke gabashin kasar Congo inda ake hakar ma'adanai a gabashin kasar da ya shahara wajen samar da wani muhimmin ma'adinan da ake amfani da su a wayoyin salula na zamani, a cewar kungiyar a ranar Alhamis.
Wani jami'in Amurka ya fada a ranar Alhamis cewa Rasha ta tura wasu sojojinta zuwa wani sansanin sojin sama a Jamhuriyar Nijar inda wasu 'yan tsirarun sojojin Amurka suka rage bayan da akasarin sojojin Amurka suka fice daga sansanin da ke Yamai babban birnin kasar.
Wata matsalar jinkai na kara ta'azzara a arewa maso gabashin kasar Mali inda kungiyoyi masu dauke da makamai da ke da alaka da kungiyar IS suka yi wa manyan garuruwan kawanya.
Kungiyoyin kwadago sun bayyana irin bukatunsu da sukace suna fafutukar ganin gwamnati na samar musu da wata mafita wanda zai dace da halin matsin da ake ciki a yanzu a Nijar.
Kamfanin Majik Water yana amfani da na’urar da aka kera a Indiya, wacce ke zakulo tururi daga iska ta amfani da matatar lantarki. Da wannan fasahar, ana iya samar da ruwa kimanin lita 500 a kowace rana a yankunan da ba su da ruwa.
Sojojin kasar Mali sun kashe Abu Huzeifa, kwamandan kungiyar Da'ish a yammacin Afirka, a wani gagarumin farmaki da suka kai a yankin Menaka da ke arewacin kasar, a cewar sanarwar da hukumomin Malin suka karanta a gidan talabijin din kasar a ranar Litinin din nan.
Ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa sun ratsa ta gidaje tare da katse wata babbar hanya a kasar Kenya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 45 tare da bacewar wasu da dama a ranar Litinin din nan, in ji ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar.
Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da gwamnatocin Burtaniya da Amurka suka fitar ta yi Allah wa dai da kashe-kashen fararen hula da aka yi a kasar Burkina Faso.
A ranar Litinin ne ake gudanar da zaben ‘yan majalisar dokokin kasar Togo bayan wani garambawul na kundin tsarin mulkin kasar, wanda ‘yan adawa ke cewa shi ne ya share fage ga shugaba Faure Gnassingbe na tsawaita mulkin iyalansa na tsawon shekaru da dama.
Yarima Harry da matarsa Meghan za su ziyarci Najeriya a watan Mayu don tattaunawa kan wasannin Invictus, wanda ya kirkira don taimakawa tsoffin sojoji da wadanda ke kan aiki masu raunuka don su samu lafiya, in ji wani jami'in Najeriya a ranar Lahadi.
Matakin da Hukumar ta CSC ta dauka ya hada da bada umarnin dakatar da sake yada rahoton nan take tare da dakatar da shirye-shirye kafafen yada labaran kasa da kasar 2 tsawon makonni 2.
Domin Kari
No media source currently available