Zaben tsakiyar Wa'adin Shugaban Kasa A Amurka

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattijan Amurka, Harry Reid, yana cikin wadanda suke fuskantar kalubale sosai daga 'yan jam'iyyar Republican masu neman kwace wannan kujera. A nan yana jawabi ne wajen kyamfe a birnin Las Vegas a jiharsu ta Nevada.

Shugaba Barack Obama ranar asabar 30 Oktoba yana kyamfe wa 'yan jam'iyyarsa ta Democrat a Chicago, Jihar Illinois.

Ma'aikata a wani ofishin 'yan Democrat su na buga waya don neman magoya bayansu da su fita zabe ranar talata 2 Nuwamba 2010

Shugaban jam'iyyar Republican a Jihar New Hampshire kuma tsohon gwamna John Sununu a wajen wani gangami ran 22 Oktoba, 2010 a birnin Concord.

Wani dan Republican a Jihar Hawaii yana kyamfe ma kansa

Shugaban 'yan Republican a majalisar wakilai, John Boehner (a tsakiya) yana kallon shugaba Barack Obama (hagu) yana magana da shugaban 'yan Democrat a majalisar wakilai, Steny Hoyer.

Sarah Palin, wadda ta yi takarar mataimakiyar shugaban kasa ma jam'iyyar Republican a zaben 2008, tana yakin neman zabe ma 'yan tsananin ra'ayin rikau na jam'iyyar wadanda ke kiran kansu 'yan Tea Party

Shugaban marasa trinjaye a majalisar wakilai 'yan Republican, John Boehner, wanda ke fatar zamowa kakakin majalisa idan 'yan Republican sun kwato wannan majalisar daga hannun 'yan Democrat a ranar talata, 2 Nuwamba 2010

John Boehner na jihar Ohio, shugaban 'yan Republican na majalisar wakilan tarayya

Shugaba Barack Obama, yana kyamfe ma 'yan jam'iyyarsa.

hausawa suka ce ba a san maci tuwo ba, sai miya ta kare.

Hotuna daga kowace kusurwa ta Amurka dangane da yakin neman zaben 'yan majalisar dokokin tarayya da za a gudanar Talata, 2 Nuwamba, 2010.