No media source currently available
Mutane a Ghana su na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu a game da sabon bashin da gwamnatin kasar ta ciwo daga IMF na dala biliyan 3 a makon jiya.
A cewar wata kungiyar kasa da kasa mai zaman kanta da ake kira ONE, a 2021, yawan bashin da ake bin kasashen Afirka ya kai dalar Amurka biliyan 644.9. Kungiyar ta kara da cewa a karshen wannan shekara ta 2023, kasashen Afirka za su biya dalar Amurka biliyan 68.9 na basussuka
Shin wane alfanu ko rashin alfanu ne basussukan da kasashen Afirka ke karbowa daga IMF da Bankin Duniya ke da shi ga tattalin arzikin kasashen?
Wasu masu sharhi dai na danganta hauhawar farashin kayan masarufi a Najeriya akan faduwar darajar kudin kasar da kuma yawan basussukan da kasar ke ciyowa.