Ana sa ran samar da karin allurar riga-kafin cutar COVID-19 zai taimaka wajen farfado da karfin tattalin arzikin duniya a wannan shekara, a cewar wani hasashe da hukumar ba da lumani ta IMF ta yi a ranar Talata.
Hukumar kula da hakkoki da karfafa gwiwar ‘yan kasa akan harkokin albarkatun mai da Iskar gas ta Najeriya ta ce damar da kamfanonin cikin gida masu hada-hada a bangaren albarkatun mai na kasar sun karu da kimanin kashi 30 cikin dari.
Duba da irin alfanun da albasa ke da shi a jikin bil'adama da kuma irin tashin gwauron zabi da farashinta ya yi a Najeriya, wanda ba a taba gannin irinsa ba a tsawon lokaci ya sa aka kafa sabuwar kungiyar ‘yan kasuwa ta masu sarrafa albasa ta kasa.
A ranar Litinin hukumomi a kasar Italiya sun ci tarar kamfanin Apple Euro miliyan 10, kimanin dala miliyan 12.