An Yi Jana'izar Wadanda Harin Ranar Kirsimeti A Unguwar Madalla Ya Rutsa Da Su
Jana'izar Mutanen Da Aka Kashe A Madalla
Mata kenan ke kuka a yayin jana’izar bai daya ta wadanda su ka rasu a harin bam din ranar Kirsimeti a majami’ar Katolika ta St. Theresa.
Limaman coci kenan ke jagorantar addu’o’i yayin jana’izar wadanda aka kashe a harin bam din na Madalla.
Jama’a na kallo a yayin da ‘yan kungiyar agajin Boys Scouts ke dauke da akwatunan gawarwakin wadanda aka kashe a harin.
Limaman coci kenan a harabar makabartar wadanda aka kashe a harin.
Wasu mata kenan ke nuna alhini a lokacin jana’izar bai daya ta wadanda su ka rasu a harin bam din ranar Kirsimeti a majami’ar Katolika ta St. Theresa.
Wata mace kenan ke ta kuka a yayin jana’izar bai daya ta wadanda su ka rasu a harin bam din ranar Kirsimeti a majami’ar Katolika ta St. Theresa din.