VOA60 Afirka - Januwaru 04, 2013

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan bindiga sun kasha mutane hudu, kuma sun kona ofishin jami’an tsaro a arewa maso gabashin Najeria, yankin da kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram tafi karfi. A janhuriyar Africa ta Tsakiya, hankali ya fara kwanciya a babban birnin Bengui bayan da ‘yan tawaye suka yarje ma tattaunawar sulhu. Yayinda bukatar Karo ke karuwa a fadin duniya, kasar Sudan ta fara hada-hadar sa, saboda albarkatun bishiyun Karon da take da shi. A Africa ta Kudu, yau take ranar farko da Benon Lutaaya, mai zane kuma haihuwar kasar Uganda, yake nuna wa duniya aikinsa, kuma ya samu yabawar mutane. Mutanen kasar Mali na fata kungiyar kwallon kafarsu da ta kunshi yara zalla, zata yi wani abun arziki a gasar kwallon kafa ta nahiyar Africa ta shekarar 2013.