Amurka Zata Bayar Da Tukuicin Dala Miliyan 7 Don Kamo Abubakar Shekau

Imam Abubakar Shekau a tsakiyar wasu mayaka na Kungiyar Boko Haram

A karon farko, Amurka ta ce zata bayarda tukuicin miliyoyin daloli ga wadanda zasu taimaka wajen kamo wadanda ake tuhuma da ta'addanci a Afirka ta Yamma
A karon farko, Amurka tana tayin bayarda tukuicin kudi mai yawa domin kamo mutanen da ake zargi da laifin ayyukan ta'addanci a Afirka ta Yamma.

A ranar litinin, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta kebe dala miliyan 23 domin bayarwa tukuici ga wadanda zasu taimaka wajen bayar da bayanan da zasu kai ga kamo mutane biyar da aka fi nema a yankin na Afirka ta yamma.

Tukuici mafi tsoka na dala miliyan har 7, watau fiye da Naira miliyan dubu daya, an ware shi ne domin bayarwa ga wanda zai bayar da bayanin da zai kai ga kamo shugaban kungiyar nan ta Boko Haram, Abubakar Shekau. Kungiyar tana da cibiya a Najeriya, kuma ta dauki alhakin hare-hare da dama a kasar, ciki har da harin da aka kai kan ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Abuja a shekarar 2011.

Har ila yau daga cikin wadanda aka yi tayin tukuici domin kamowa har da Mokhtar Belmokhtar, wanda ya dauki alhakin wani farmakin da aka kai cikin wannan shekara a kan wata masana'antar gas ta kasar Aljeriya. Belmokhtar shi ne shugaban kungiyar nan da ake kira "al-Mu'aqi'oon Biddam" (Masu rubutu da jini), kuma tsohon shugaban kungiyar al-Qa'ida ta yankin Maghreb ce.

Sauran wadanda za a bayarda tukuuici ga wanda ya taimaka aka kamo su sune Yahya Abu el-Hamman da Malik Abou Abdelkarim 'ya'yan kungiyar al-Qa'ida ta yankin Maghreb da kuma wani tsohon dan kungiyar, Oumar Ould Hamaha, wanda a yanzu shi ne kakakin kungiyar nan ta MUJAO.