Nijar Tana Farautar Fursunoni Masu Alaka Da Ta'addanci

Soojin Nijar tsaye a kofar babban gidan kurkukun Yamai, a bayan wani farmakin da ya janyo mutuwar mutane da dama, da kuma tserewar wasu fursunonin wadanda ake tsammanin su na da hannu a ayyukan ta'addanci.

Kwanaki biyar bayan farmakin da aka kai kan babban gidan kurkuku na birnin Yamai, gwamnatin Nijar ta fito da hotunan mutane 9 masu alaka da ta'addanci da suka tsere
Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun fito da hotunan wasu mutane 9 da suka ce masu alaka da ayyukan ta'addanci ne, wadanda suka balle daga gidan kurkukun birnin Yamai a lokacin wani farmakin da ya kashe fursunoni 22 a ranar asabar da ta shige.

Wakilin Sashen Hausa, Abdoulaye Mamane Ahmadou, yace daga cikin mutanen 9 da ake nema ruwa a jallo, har da wani mutumi mai suna Chebani, wanda ya taba kashe Ba-Amurke daya da wasu larabawa 'yan kasar Saudi Arabiya su 4.

Mahukuntan Nijar, su na fata bayyana wadannan hotuna, zasu taimaka musu wajen ba jama'ar kasar damar sanya hannu a farautar wadannan mutane da ake yi.

Ga cikakken rahoton Abdoulaye daga birnin Yamai

Your browser doesn’t support HTML5

Rahoto Daga Nijar Kan Mutanen Da Suka Gudu Daga Kurkuku, Ake Kuma Nemansu - 2'53"