Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa Ya Cika Shekara 48 Da Rasuwa Yau

Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa

Sir Abubakar Tafawa Balewa, Firayim ministan Najeriya na farko

Sarauniya Elizabeth II ta Ingila tana gaisawa da Abubakar Tafawa Balewa, ministan sufuri na Najeriya a ranar 10 Fabrairu 1956, a bayan bude sabuwar tashar ruwan Apapa a Lagos. A tsaye a bayan sarauniyar, gwamna-janar na Najeriya ne, Sir James Robertson.

An dauki wannan hoto ranar 27 Satumba, 1960, kwanaki kadan kafin ranar 'yancin Najeriya, kuma ya nuna Firayim minista Abubakar Tafawa Balewa, tare da Gimbiya Alexandra ta Kent, da gwamna-janar na Najeriya mai barin gado, Sir James Robertson, lokacin wata hira da 'yan jarida a gidan gwamnati a Lagos. Gimbiya Alexandra ta Kent ita ta wakilci Sarauniya Elizabeth II a lokacin bukukuwan 'yancin kan Najeriya.

Firayim Minista Abubakar Tafawa Balewa tare da Gimbiya Alexandra

Gimbiya Alexandra ta Kent, tana karanta sakon Sarauniya Elizabeth II a dandalin Royal Pavilion, a filin sukuwa na Lagos, ranar 1 Oktoba, 1960. Firayim ministan tarayyar Najeriya, Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa, zaune a dama, yana sauraron jawabin nata.

Shugaba William Tubman na Liberiya tsaye yana jawabi a wajen wata liyafar da gwamnatin Najeriya ta shirya a Federal Palace Hotel dake Lagos ranar 26 ga watan Janairu, 1962. Firayim minista Abubakar Tafawa Balewa yana zaune a dama cikin hoton. Sauran wadanda suke ciki sune (daga hagu zuwa dama) Mrs. Flora Azikiwe, matar Dr. Nnamdi Azikiwe, gwamna-janar na Najeriya; da Sarkin Sarakuna na Habasha, Haile Selassie; sai Dr. Nnamdi Azikiwe.

Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa