Hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA, ta dakatar da dan wasan Uruguay Luis Suarez na wasanni 9, ta kuma haramta masa shiga duk wata harkar kwallon kafa na tsawon watanni 4 a saboda cizon da ya gantsara ma Girgio Chiellini na kasar Italiya a lokacin da suke karawa a gasar cin kofin duniya.
Har ila yau, Suarez zai biya tarar kimanin dala dubu 112 (kimanin naira miliyan 18 da rabi). Ba za a bar shi ya shiga filin wasa don kallon kwallon da Uruguay zata buga da Colombia jibi asabar ba, haka ma ba za a bar shi ya shiga duk wani filin da za a buga kwallon kafa a fadin duniya na tsawon watanni 4 ba.
Wannan dakatarwa ita ce mafi tsawo a tarihin gasar cin kofin duniya, domin ta zarce wasanni 8 da aka dakatar da dan wasan Italiya mauro Tassotti a 1994 a lokacin da ya fasa ma wani dan wasaan Spain mai suna Luis Enrique hanci da guiwar hannunsa.