WASHINGTON, DC —
Rahotanni daga Jihar Borno na fadin cewa 'yan bindigar da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun kai farmaki kan garin Damboa, inda suka kona sansanin soja da ofishin 'yan sanda, da babbar kasuwar garin kurmus.
Mazauna garin suka ce an kashe sojoji 12, ciki har da kwamandansu, da 'yan sanda 4 cikinsu har da DPO na Damboa, da kuma fararen hula 4.
An fara kai harin tun karfe 5 na yamma har zuwa karfe 2 na dare, watau tsawon awa 9 in ji mutanen garin na Damboa.
A kasance da Dandalin VOA domin jin karin haske kan wannan harin.