Mahara Sun Kashe Mutane Akalla 22 A Kenya

'Yan sanda tsaye kusa da wata motar da aka kona lokacin da 'yan bindiga suka kai farmaki yau lahadi a kofar caji ofis na Gamba a kasar Kenya

Kungiyar agajin Red Cross ta Kenya ta ce mahara sun kashe mutane akalla 22 a wasu kananan hukumomi biyu dake bakin gabar teku a Kenya, ciki har da wani yankin da tsagera suka kashe mutane 65 a watan da ya shige.

Kungiyar al-Shabab mai alaka da al-Qa'ida ta dauki alhakin hari na baya-bayan nan kamar yadda ta ce ita ce ta aikata kisan gillar watan da ya shige.

Jami'ai sun fada yau lahadi cewa wasu mutane kimanin dozin daya (12) suka kai wadannan hare-hare cikin dare a kananan hukumomin Lamu da Tana.

Daga cikin wadanda aka kashe a wani harin da aka kai a kan caji ofis na 'yan sanda har da fursunoni da dama da kuma wani dan sanda.

Kenya ta fuskanci hare-haren bam da na 'yan bindiga a lokuta da dama tun lokacin da gwamnatin kasar ta tura sojoji cikin Somaliya domin yakar al-Shabab a shekarar 2011.