Hukumar Zabe ta Najeriya, ta Gudanar da Wasu Canje-Canje

Wata mata tana jefa kuri'a a Najeriya

Hukumar zabe ta Najeriya, ta gudanar da wasu canje-canje da ya shafi karban katunan ragistan masu zabe a ciki kasar.

Huklumar ta dage shirye-shiryen da tayi ada daga watan nan na yuli zuwa watan Augusta wanda ake sa ran ‘yan kasa daban-daban daga jihohi guda goma na farko zasu fara karkan katunansu na zabe na dindindin a cikin Najeriya.

Yanzu dai ‘yan kasa sun tukufa domin yin amfani da wannan lokaci sabo da hukumar zabe ta fitar domin wadanda basu da katunan zabe ko kuma suke da matsaloli da katunan su a yanzu su tabbatar ganin cewa sunyi amfani da wannan damar domin warware matsalar.

Domin ta hanyar gada kuri’a ne kawai ‘yan kasa zasu iya damar da suke da ita na canja ko kuma tabbatar da shuwagabaninsu dake mulki a yanzu.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar zabe ta kasa - 3'36"