Kontagora Zata Samu Makarantar Unguwarzoma

Ma'aikatan Ungwarzoma

Gwamnatin jihar Nejar, ta fara aikin samar da wata makarantar, koyar da aikin ungwarzoma, agarin kontagora, dake cikin jihar.

Gwamnatin jihar tace hakan na daya daga cikin matakan da take dauka na samar da kwararun ma’aikatan kiwon lafiya domin rage mace-macen mata a wurin haihuwa masammam a wannan yanki.

Dr. Muhammad Bashar, kwamishinar maikatan ilimi mai zurfi a jihar, yace Mallamai na kiwon lafiya yanzu basu wadata a koina ba samu irin wadannan makarantun zai taimaka wajen tanadar da kiwon lafiya masammam na mata da jarirai da wajen haihuwa.

Alumar yankin na Kontagora dai sun ce sunyi maraba da wannan mataki alamarin da suka ce wani ci gaba ta fanin kula da lafiyan yankin.

Your browser doesn’t support HTML5

Kontagora Zata Samu Makarantar Unguwarzoma - 2'57"