Sojojin Najeriya Sun Kama Wasu 'Yan Arewacin Najeriya a jihar Imo

'Yan arewa

Jami’an tsaro sojojin Najeriya, sun kama wani Limamin Masallacin Jumu’a da wasu shuwagabani su goma sha uku a garin Aba na jihar Abia, bisa zargin su da boye wasu dimbin makamai.

An kama mutanen nea wani samame da rudunar soja Najeriya suka kai a Masallatai da wasu kasuwani da ‘yan arewacin Najeriya, ke gudanar da harkokin su a birnin na Aba.

Jami’an tsaron na kuma zargin mutanen da boye Boma-Bomai a sassa daban-daban da ‘yan arewacin Najeriya, ke gudanar da harkokinsu.

Mallam Bashir Idris, babban Limamin Masallacin juma’a na garin Aba, kuma daya daga cikin wadanda aka kama yace “ mu dai abunda ya bamu mamaki shine jami’an tsaro na soja sun yima diran mikiya tare da farma Masallacin, kan wani bincike Alhamdulillahi suka bincika basu sami koda reza ba, sun kuma shiga gida na da na Naibi na baa bun da suka samu sai suka koma sama makarantar yara inda ake koyarda Islamiya da kuma ilimin zamani anan suka shiga wani daki wanda ake binciken kimiya suka samu wasu ‘yan kwalabe shine suka tattara suka ce wai da shine muke hada boma-Bomai a Masallaci."

Your browser doesn’t support HTML5

Bincike a Masallaci - 3'24"