Sojojin Israila sun ce sun kakkabo wata na'ura mai tashi sama, wadda ta shiga sararin samaniyar Israila daga Gaza.
A yau litinin wani kakakin sojojin ke cewa na'urar na tafe a sararin samaniya ta na shawagi a saman birnin Ashdod, da ke tsakanin Zirin Gaza da Tel Aviv, a wannan lokaci ne sojojin Israila su ka cilla ma ta makamai masu linzami.
Haka kuma sojojin Israila sun ce mayakan Hamas sun harba dimbin rokoki a yau litinin daga Gaza, a yayin da cikin dare jiragen saman yakin Israila suka yi ruwan wuta kan dimbin wurare a Gaza.
Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya bayyana damuwa game da tashin hankalin da ke faruwa, sannan ya bukaci da lallai bangarorin biyu su dauki matakan kawo karshen fadan nan take.
Mr.Ban ya cewa rokokin da Hamas ke harbawa cikin Israila sun karya dokar kasa da kasa, amma kuma ya ce hare-haren Israila sun hallaka dimbin Falasdinawa.
Jami'an Falasdinawa sun ce tun da Israila ta kaddamar da kai hare-hare ranar talatar da ta gabata, ta kashe mutane fiye da dari da sittin da suka hada da 'yan tawaye. Amma aka ce akasarin wadanda ta kashe fararen hula ne.
Kungiyar kasashen Larabawa ta yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakin kawo karshen hare-haren da Irsaila ke kaiwa, kungiyar ta ce ba za ta yiwu ba, a ci gaba da yin gum da baki, ana tsura ma ta ido. Akwai bukatar kungiyar kasashen Larabawan da kugiyoyin ayyukan agajin jin kai su kiyaye lafiyar al'ummar Falasdinawa.