Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya Yayi Kira aTsagaita wuta a Zirin Gaza

Wani Uba da 'yayansa Falasdin

Kwamitin Sulhun Majalisar dinkin duniya yayi kira a tsagaita wuta a Zirin Gaza sata-izan, sannan ya bayyana damuwa game da yadda tashin hankali ya kazance a can, a daidai lokacin da Israila ke kara matsa kaimin kaiwa 'yan tawayen Hamas hare-hare ta sama da ta kasa.

Kwamitin ya gabatar da sanarwa da yammacin jiya lahadi bayan yayi wani zaman gaggawa da jakadan kasar Rwanda kuma shugaban Kwamiti na yanzu, Eugene Gasana, ya bayyana da cewa zama ne mai sawa a yi tunani. Kwamitin ya kara jaddada bukatar kyautata ayyukan agajin jin kai da suka hada da kiyaye lafiyar fararen hular.

Tun da aka fara fadan kusan makonni biyu kenan, ranar jiya ta lahadi ita ce mafi muni, inda Falasdinawa 65 a kalla suka mutu, gami da sojojin Israila 13 da kuma wasu Amurkawa biyu.

Jakadan Falasdinu a Majalisar dinkin duniya, Riyad Mansour ya ce shi da wadanda yake wakilta sun zaci Kwamitin Sulhun zai samar da kudirin yin tofin Allah tsine da ahir ga harin da ake kaiwa al'ummar shi, sannan kuma a zartas da wani matakin kare lafiyar su nan take.