Mummunar tsamar dake tsakanin Seydou Keita dan kasar Mali mai buga ma AS Roma, da Pepe dan kasar Portugal, mai buga ma Real Madrid, ta sake kunno kai a wasan sada zumuncin da kungiyoyinsu na yanzu suka buga a Dallas dake Jihar Texas a nan Amurka.
A lokacin da aka fara wannan tsama a 2011, Keita yana buga ma FC Barcelona yayin da shi Pepe ke buga ma kungiyarsa ta yanzu, Real Madrid.
A wasan sada zumuntar na Dallas, Keita yace shi ba zai yi hannu da Pepe ba, har ma ya dauki kwalbar ruwa ya jefe shi da ita. Wani jami'in wasan yace shi kuma Pepe ya tofa ma Keita yawu. Wannan ya so ya hautsina wasan tun ma ba a fara shi ba, amma a bayan da aka tattauna a tsakanin Keita da Xabi Alonso, an kwantar da hankula aka buga kwallo.
Keita yana zargin Pepe da cewa ya kira shi da sunan Biri a lokacin da suke wasan cin kofin Supercopa na Spain a shekarar 2011.