Manchester United Tayi Targade A Wasanta Na Farko Na Firimiya Lig A Bana

Wayne Rooney na Manchester United

Yau aka bude sabuwar kakar kwallon kafa ta Firimiya Lig a kasar Ingila, amma kuma wasan farko da ‘yan Manchester United suka yi a gida karkashin sabon manaja Louis van Gaal, bai tafi yadda suka so ba, domin kuwa kungiyar ta sha kashi a hannun Swansea da ci 2-1.

Wannan shi ne karon farko a tarihi da kungiyar Swansea take samun nasara a kan Manchester United a gida ko a waje. Haka kuma, wannan shi ne karon farko da Manchester United take shan kashi ranar bude wasa a gidanta tun shekarar 1972, watau shekaru 42 da suka shige.

A sauran wasannin na yau, Arsenal ta doke Crystal Palace da ci 2-1, Aston Villa ta doke Stoke City da ci 1-0, Tottenham ta doke West Ham United da ci 1-0.