Wani sojan Najeriya da bai yarda fadi sunansa ba, yace ya sadaukar da kansa ga yakar 'yan Boko Haram ne a saboda babu abinda suke yi na Musulunci in ban da bata sunan addinin Musulunci, da nakkasa yankin arewacin Najeriya, da kuma nakkasa kasar baki daya.
A cikin hirar da yayi da Dandalin VOA, wannan sojan dake bakin daga, yace a duk lokacin da Boko Haram ta kai farmaki ko aka fara yaki da ita, yaran mutane da ta kama ta tilasta musu shiga cikinta ta hanyar tsafe-tsafe, sune aka tura keyarsu gaba a yi ta kashe su, yayin da ainihin 'yan kungiyar ke boye a can baya sai idan wuri yayi wuri suke fitowa.
Sojan yace sojojin bataliyarsu su wajen 200 sun tsallaka cikin Kamaru kwanakin baya, amma ba su da alaka da daruruwan sojojin da suka shyiga Kamaru daga wani fadan a Gamboru-Ngala. Yace dalilinsu na tsallakawa kuwa shi ne, harsasansu en suka kare kafin a kai musu dauki, amma daga baya sun koma sun gwabza da mayakan Boko Haram a Pulka, kan hanyar zuwa Gwoza.
Sojan yace har yau har gobe su na da niyyar aikin sojan nan, ba zasu bari ba, yana mai bayyana 'yan Boko Haram a zaman marasa imani na kowane irin addini ma.
Ga cikakken bayaninsa.
Your browser doesn’t support HTML5
Wani Sojan Najeriya - Manyan Dalilai Na Uku Na Yakar Boko Haram - 3'32"