Lauya dan rajin kare hakkin bil Adama da yaki da zarmiya da cin hanci, Barista Solomon Dalung, yace wasu 'yan Kudu ne suke amfani da rikicin Boko Haram a yanzu, suke kara rura wutarsa, domin cimma gurorinsu na siyasa.
Barista Dalung yayi misali da bam na farko da aka fara tayarwa a Abuja a ranar 1 Oktoba na 2010, wanda Henry da Charles Orkar suka dauki alhakin kaiwa, amma shugaba Goodluck Jonathan yayi maza yana cewa ba su ba ne.
"John Odeh, wanda ya shugabanci hare-haren da aka kai wa Coci a Kaduna, John Odeh ba dan Arewa ba ne, mutumin south-south (yankin kudu da ya kumshi jihohin kabilar Igbo) ne," in ji Barista Dalung.
Ya kara da cewa, "yara 400 da aka kama a bakin daga a (Jihar Borno) kwanan nan, dukkansu mutanen kudu ne."
Barista Dalung yace da farko Boko Haram ta fara a zaman kungiyar addini, amma a yanzu, 'yan kudu sun karbe ta sun maida ta ta cimma siyasarsu.
Yayi misali da zargin da Rev. Stephen Davies mai shiga tsakani domin sako 'yan matan Chibok, kuma dan kasar Australiya, yayi cewa yara ukun da suka kai hari a Nyanya, sun fito ne daga gidan tsohon babban hafsan hafsoshin sojan kasa na Najeriya, Janar Ihejirika mai ritaya.
Your browser doesn’t support HTML5
'Yan Kudu Ne Ke Gudanar Da Boko Haram Yanzu In Ji Barrister Dalung - 1'24"