WASHINGTON, DC —
Rahotanni daga Kano sun ce an kai wani harin da ake kyautata zaton na bam ne a Kolejin Horas da Malamai ta Tarayya, FCE, dake cikin birnin Kano.
Har yanzu babu wani takamammen rahoto na hasarar rayuka ko jin rauni, amma kuma akwai fargabar cewa an kashe dalibai da dama.
Haka kuma babu tabbas a kan ko su wanene suka kai harin, amma ana kyautata zaton cewa aiki ne na kungiyar Boko Haram.
A kasance da DandalinVOA domin jin cikakken bayani.