Tuna Baya: Taron Tsarin Mulkin Najeriya Na 1957 A Ingila

Wannan hoto na sama da ake gani, na manyan wadanda suka gabatar da jawabai ne a ranar da aka bude taron Tsarin Mulki na Najeriya a Lancaster House dake London, ranar 23 Mayu, shekarar 1957, watau shekaru 3 kafin Najeriya ta samu 'yancin kai.

Daga hagu zuwa dama a wannan hoto, Firimiyan Yamma, Cif Obafemi Awolowo; sai Sakatare Mai Kula Da Kasashen dake karkashin mulkin mallaka na Ingila, Alan Lennox Boyd; sai Firimiyan Arewa, Alhaji Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato; sai Gwamna-Janar na Tarayyar Najeriya, Sir James Robertson; sai kuma Firimiyan Gabas, Dr. Nnamdi Azikiwe.

A wurin wannan taro na Lancaster House aka tattauna kan irin tsarin mulkin da kasar Najeriya zata yi amfani da shi idan ta samu 'yancin kanta.