Jiya Ba Yau Ba: Sarauniyar Ingila A Kaduna A Shekarar 1956

Allah Sarki, jiya ba yau ba. A hoto na sama, Sarauniya Elizabeth II take duba masu sakar huluna da jaka, ranar 3 Fabrairu, 1956 a Kaduna. Tare da Sarauniyar ta Ingila, akwai Makaman Bida, ministan Ilmi na Tarayya a hagu, sai kuma Sardaunan Sakkwato, Firimiyan Jihar Arewa.