Sama da Yara Miliyan Biyu ne Za’a Yiwa Rigakafin Cutar, Shan Inna a jihar Neja
Ana digawa wata jaririya maganin rigakafi
WASHINGTON, DC —
Sama da yara miliyan biyu ne za’a yiwa rigakafin cutar, shan Inna, a jihar Neja, a zagayen karshe na wannan shekaran.
Jami’an, kiwon lafiya, a jihar, dai sun ce sun yi shiri,domin tabbatar da ganin cewa ba’a , samu matsala ba, a lokaci, bada rigakafin, da za’a, fara a yau asabar.
Gwamnatin jihar Neja, ta ware kwanaki hudu domin aiwatar da aikin yiwa yara rigakafi
A halin yanzu dai guragun da cutar shan inna ta nakasa, a jihar Neja, sun ce har yanzu, suna samun matsalar tsangwama, da nuna wariya daga jama’a, a sakamakon kamuwa da wannan cutar, inji Malam Auwal Ahamed, shugaban guragun jihar ta Neja.