Ana Wata Ga Wata - Garkuwa Da Mutane A Paris

Jiragen helkwafta dauke da zaratan sojojin kundumbala na Faransa a saman inda 'yan bindiga suka buya suke garkuwa da akalla mutum guda.

Jami'an tsaro a Faransa sun killace wurin da 'yan bindigar nan da ake zargi da kashe mutane 12 a gidan jaridar zambo ta Charlie Hebdo, suka buya su na yin garkuwa da akalla mutum guda.

Ana cikin wannan kuma, sai wani dan bindigar ya shiga wata kasuwar sayar da kayan cefane na yahudawa a birnin Paris inda yayi garkuwa da mutane kimanin biyar. Ana kyautata zaton cewa wannan dan bidniga shi ne ya kashe wata 'yar sanda a birnin na Paris a jiya.

Dandalin VOA ya tattauna da wani dan jarida dake zaune a birnin Paris, Sadiq Abba Mamadou, wanda ya bayyana halin da ake ciki yanzu haka a can.

Your browser doesn’t support HTML5

Farautar 'Yan Bindiga A Paris-Abba Sadiq Mamadou - 6'11"