Wutar Lantarki Ginshikin Kasuwanci da Rayuwa

Wutar Lantarki

Wutar lantarki wata babbar abuce a rayuwar dan’adam baki daya, a kasashen da suka cigaba wutar lantarki bata taba zama abun magana akai ba. Masana naganin cewar duk kasar da ta iya magance matsalar wutan lantarki, to babu shakka wannan kasar zata iya zama wata abun koyi a duniya.

Harkokin cinikayya a tsakanin kasashe masu makotaka da juna wani abune da kan iya samar da kakkyawar dangantaka. Mutane da dama kan baro kasashen su a yankin Afrika maso yamma don zuwa wasu kasashen, da niyyar habbaka kasuwanci, amma a wasu lokutta akansamu wasu matsaloli da kan haifar da koma baya a wannan harkar kasuwancin.

A tabakin wata mata da kan kai kawo a tsakanin kasar Ghana da Najeriya, a harkar kasuwanci, tace sukanzo cikin Najeriya, su sayi kaya su kai kasar Ghana, don siyarwa, amma yanzu saboda matsalar wutar lantarki da matsalar manfetur wannan yana shafar kasuwancin su matuka.

Wanna yana neman yasa sana’ar tasu cikin halin ha’ula’I, a sanadiyar basu samu damar karban kudaden su a banki ba, saboda wasu dalilai na rashin ingantaciyar wutar lantarki dama wasu abubuwan more rayuwa a kasar.

Don haka suna ganin lallai ta inganta abubuwan more rayuwa da yakamata ace kowane dankasa yasamu batare da wasu matsaloliba, shine kawai hanya da za’a samu cinma nasara a kowace irin harka a duniya bama kawai sai ta kasuwanci ba.