Yaran Masu Gudun Hijira Sun Chan-chan ci Kulawar Musamman

Hoton Sabon Shugaban Najeriya, MuhammadBuhari Da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osibanjo

A irin cigaba da yunkurin da sabuwar gwamanatin Najeriya keyi, wajen yaki da ta’addanci da talauci a kasar. Mataimakin shugaban kasar Farfesa. Yemi Oshibanjo, ya kai wata ziyar aiki a jihar Kano. Inda ya ziyarci makarantar da aka kai yara samada dari da ashirin wadanda suke ‘yayan ‘yan gudun hijira ne da aka dauko daga jihar Borno, don basu damar samun nagartacen ilimi dai dai da kowane yaro.

A cikin jawabin shi yayi godiya ga gwamnatin jihar Kano, da wannan yunkuri, kuma ya bama wadannan yaran tabbacin cewar gwamnatinsu, bata manta da suba, kuma suna kokarinsu wajen ganin sun samamusu duk wasu abubuwa da yakamata, don more rayuwarsu kamar kowane yaro a kasar. Sai yakara dacewar gwamnatinsu ta samar da wata gidauniya wadda Ganaral T.Y Danjuma mai murabus kema jagoranci, kuma wanna kwamirtin zai kokarta wajen inganta rayuwar wadannan yaran dama iyayensu.

A tabakin mataimakin gwamna jihar Kano, Farfesa Hafizu Abubakar, yace wadannan yaran sun chanchanci kulawa kashi biyu, da na harkar rayuwar yauda kullun, da kuma ta abunda yashafi kwakwalwarsu, don haka gwamnatinsu a shirye take ta ga ta samama wadanna yara duk abubuwan da suka kamata. Suma dai yaran sun bayyanar da irin jin dadinsu ganin mataimakin shugaban kasa bai manta dasuba, sunji dadi kuma suna fatar Allah ya karayima wanna gwamnatin jagoranci baki daya.