Kwazon 'Yan-Makaranta Na Wajen Kulawar Malamai

Yara 'yan makaranta

An gudanar da wani bincike a jihar Tennesse, ta nan kasar Amurka, wanda ya bayyanar da cewar hanyoyin da za’a bi don kara bama yara dalibai ‘yan makarantar firamari da sakandire. Kwarin gwiwa wajen kwazo a karatun su, musamman ma yaran da suka fito daga gida mai talauci shine.

Da akwai bukatar malamai su dinga ziyartar wadanna daliban a gidajen iyayen su, lokaci zuwa lokaci. A furucinta, shugaban makarantar Hobgood Elementry School. Mrs. Tammy Garrett a karamar hukumar Mufreesboro. Idan har malamai sun san halin da yara da suka fito daga gidajen masu karamin karfi suke, to lallai wanna shi zai basu masaniyar wane irin hali wadanna yaran, suke samun kan su. Kuma wanna shi zai sa malaman su fahimci dalililan da suke sa wadanna yara basu samun damar gudanar da aikin gida da ake basu a kowane lokaci a makaranta.

Sai ta kara da cewar wadanna yaran da suka firo daga irinwadanna gidan, iyayen su basu da kwanciyar hankalin da har zasu dinga duba wane irin aiki aka ba yaran a makaranta, balle har su ga cewar yaran sun yi wanna aikin yada yakamata a kan kari. Ta bada misali da cewar, a wanna gari nasu, kimanin kashi 90% na yaran da suka fito daga gida masu karamin karfi basu samun su mai da hankali wajen fahimtar karatu. Don haka akwai bukatar malamai su dinga ziyarar gidajen daliban su daga lokaci zuwa lokaci.