Doka doka ce a kan kowa, a wata makarantar gwamnati a yankin kudancin jihar New Jersey, dake kasar Amurka, jiya suka kori wata daliba ‘yar shekaru takwas 8, da haihuwa daga makaranta. Akan dalilin cewar yarinyar tasa rigar makaranta da ta yi duhu da kallar tsarin rigar makaranta ga kowane yaro.
A cewar uwar yarinyar, ai kalan da yarinyar tasa, kadanne ban-bancin su da ta makarantar, domin kuwa sun ce yara su sa riga mai kalan shudi, ita kuwa bata samu wannan kalar ba, sai ta samu wata kalar shudi amma tana da duhu kadan. Wannan shi yasa aka koro mata yarinya.
A tabakin hukumomin makarantar sun ce, barin yara su sa wani kallan kayan makaranta, zai iya zama wata hanya da yara zasu fara wasu dabi’u wanda basu da kyau, kana hakan na iya shafar karatun yara. Domin kuwa yara kan dauki wannan a matsayin hanyar nuna isa ga sauran yara.