Tito da Amanda mata da miji da aka kama su a dalilin sun saida Lasisin shiga Aljannah, ga mutane sama da dari biyu 200. Sun dai sayar da wannan katin ne akan kudi dallar Amurka $99.99 dai-dai da naira dubu ashirin 20,000. Sun yi ikirarin cewar katin an kirkire shi ne daga zinariya, haka kuma duk wanda ya siya tikitin ya sayama kanshi gurbi a gidan Aljannah.
Sun kuma kara da cewar duk wanda ke da wannan katin idan yaje bakin kofar shiga gidan Aljannah, sai kawai ya nuna katin na shi sannan abarshi ya shiga. Amma a tabakin wani jami’in ‘yan sanda yace, wannan yaudara ce kawai domin kuwa, babu yadda za’ayi ace mutun ya siyar da tikitin shiga Aljannah. Kuma wadannan mutanen sun samu wani katako ne da sukayi ma rubutu, suka kuma ce shine katin zinariyar.
A tabakin Mr. Tito, babu ruwan mu da abun da ‘yan sanda su kace, su dai sunyi katari da Annabin Allah, Annabi Isah “Jesus” a bayan wani gidan cin abinci, ya kuma umurce su da su siyar da wannan ga duk mai bukatar shiga gidan Aljannah, ranar kiyama. Don haka su suna isar da sakon da aka basu ne.