Kamfanin Facebook Zai Fuskanci Tirjiya A Kasashen Turai

آیفون هشت

Kungiyar kasashen turai “European Union” a turance, suna zargin kamfanin shafin zumunta na facebook. Da cewar hafin zumuntar na daukar bayanan sirrin mutane a shafin da bayar da shi zuwa ga gwamnatin kasar Amurka.

Wata kotu a nahirar kasashen turai din, ta bada hukuncin cewar kamfanin ba zai bada bayanan jama’a ga gwamnatin Amurka ba, a dalilin haka kotun ta sanar da kamfanin wata yarjejeniya, da suka rattabawa hannu a tsakanin kasar Amurka da daukacin kasashen turai a shekarar 2000, don mutunta juna da karrama kawancesu.

Ana zargin kamfanin da tara bayanan jama'a a dakin tara bayanan su na kasar Amurka. Kotun na ganin cewar wannan yarjejeniyar bata aiki, sun kuma kara da cewar yakamata kasashe masu zaman kansu, su haramta ma kamfanonin kasar Amurka daukar bayan jama’ar kasar su. Sun kuma bukaci kasar Amurka da ta mutunta hakkokin bil’adam, da bayanan sirrin su. Kana masu binciken asirrin kasar Amurka na shiga hurumin da ba nasu ba na binciken mutane.