Kasashen da suka cigaba a duniya, baya ga irin wadata da Allah yayi musu, sukan maida hankali a wasu abubuwa da sauran mutane, a kasashen da suke tasowa basu maida hankali akai. Wani kamfani mai suna “Sooam Bitotech” na kasar Korea ta kudu, sun fito da wata dabara hade-haden sinadarai Kare na miji da na Karya mace, wajen samun wani jinsin kare na daban a fadin duniya.
Wani abun la’akari da shi a nan shine, akwai jinsin karnuka kala daban-daban da dama, wanda za’a hada wani jinsi da na wani, don samun wani nau’in kare daban. A kasa irin ta Amurka, wasu mutane sukan bama kare mahimanci, kamar na mutun, domin kuwa lalura da wasu kanyi akan kare, ba daya take da wadda sukeyi ga mutun ba.
A zantawa da mukayi da wasu muta ne, suna cewar suna iya kashe kudi da suka kai dallar Amurka dubu dari daya, dai-dai da naira milliyan ashrin 20,000,000. A wajen hada jinsin Karen wata kasa da na wata kasa. Wata mata ta bayyana wani kare da ta siya a kan dallar Amurka $50, bayan shekaru tara da taga alamun Karen ya tsufa, sai ta sake biyan misalin naira milliyan goma sha shida da dubu dari biyar 16,500,000 don sake sayo wasu karnuka guda biyu.