Jerin Sunayen Zababbu Don Zama Ministoci A Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari

A yau ne Shugaban Majalisar Dattauwa ta Najeriya, Sanata Dr. Abubakar Bukola Saraki, ya karanta sunannakin zababbun mutane da shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya aika musu don dubawa da tanatance su a matsayin ministocin shi.

A jawabinsa, Shugaban Majalisa Saraki, ya bayyana sunannakin mutane ashirin da biyu, wadanda suka hada da Chris Ngige – Anambra, Kayode Fayemi- Ekiti, Rotimi Amaechi – Rivers, Babatunde Fashola –Lagos, Abdulrahman Danbazau, Aisha Alhassan – Taraba, Ogbonaya Onu- Abia, Kemi Adeosun –Ogun, Abubakar Malami (SAN) –Kebbi, Sen Hadi Sirika –Katsina, Barr. Adebayo Shittu –Oyo, Suleiman Adam –Jigawa, Solomon Dalong –Plateau, Ibe Kachikwu –Delta, Osagie Ehanire –Edo, Audu Ogbeh – Benue, Lai Mohammed –Kwara, Ahmed Isa Ibeto -Niger
Amina Mohammed – Kaduna, Udoma Udo-Udoma - Akwa Ibom.

Ya kuma bada sanarwar cewar ranar, Talata goma sha uku (13), ga wannan watan zasu fara tantancewar. Ku cigaba da kasancewa da DandalinVOA don samun labarai da dumi-dumin su.