Mr. Ken Olisa, dan Najeriya mai shekaru 64, ya zamo bakin mutun na farko da ya rike mukamin “Lord-Lieutenant of Greater London” wannan matsayin dake nufin wakilin sarauniyar ingila da ya hada da kananan hukumomi 32, a cikin daular kasar Ingila.
Mr. Ken, dan kasuwa ne kuma an bayyanar da shi a matsayin bakin mutun mafi karfi a masauratar Ingila. A duk shekara akan fitar da mutane dari 100, da sarauniyar Ingila ke karramawa, a shekarar 2016, Mr. Ken, na daya daga cikin mutane da zasu samu lambar yabo mai girma daga sarauniyar Ingila.
An sakama wani dakin karatu “Library” sunan Mr.Ken a jami’ar Cambridge, wadda take cikin jerin jami’o’I manya a duniya. Za’ayi wannan bukin ne a farfajiyar dakin tarihi na “Albert Museum” an kuma bayyanar da wannan a matsayin wani cigaba da kasashen Afrika, suka samu musamman ma kasar Najeriya, wanda yanzu haka yake rike da wannan kujerar ta wakilin sarauniyar Ingila.