A shirinmu na nishadi a yau mun sami zantawa da wani furodusa Garba Saleh wanda ya fara harkar fim shekaru biyar da suka gabata.
Garba Saleh yace fim din sa na Hindo shine bakandamiyarsa, kuma fim ne da ya zuba fiye da Naira miliyan goma sha takwas , a cewarsa a shekaru biyar da suka gabata a Kannywood industry babu wani fim da aka kashewa kudaden da suka kai abinda aka kashe a Hindo.
Ya kara da cewa fim Hindo ya daukaka Kannywood zuwa wani matsayi domin a cewarsa ya sami lambobnin yabo fiye da shida sakamakon fim din Hindo
Yace ya shirya fim din ne domin ya nuna tsantsan al’adar Malam Bahaushe ba tare da sanin tabbacin cewar zai maida kudin da ya kashe a shirin din ba. Amma yace haka ta cimma ruwa domin ya sami biyan bukata game da manufasa na shirya wannan fim din na Hindo, domin jama'a sun yaba da yadda fim din ya kasance, baya ga alherin da ya biyo baya.