Dakarun Amurka sun kashe ‘yan tawayen Iraqi ashirin da hudu

Rundunar sojan Amurka ta ce ta halaka ‘yan tawayen Iraqi guda ashirin da hudu wadanda suka kai hari kan rundunar a wajen birnin Bagadaza ranar Lahadi. An raunata dakarun kawance shida a fadan. Wani harin ‘yan tawayen a Kirkuk ya halaka sojan Amurka guda. An kuma kashe wani sojan Amurka da kuma wani sojan kundunbala a lokacin wani samamen jami’an tsaro a kusa da Fallujah da kuma wani wuri a gundumar Al-anbar a yammacin Bagadaza.

A birnin Mosul kuma na arewacin kasar wani dan kunar bakin wake ya kashe wani babban jami’in hukumar hana cin hanci da rashawa a wani hari da aka danganta shi da mayakan al-Qaida. Bayan awanni kadan kuma wasu ‘yan bindigar da ba a gane ko su wanene ba sun yi harbi kan wani ayarin motoci na wani wanda ya halaka sakamakon harin bama-bamai a inda aka halaka mutane biyu.

A wata sabuwa kuma, Iraqi ta kira jakadanta na Jordan zuwa gida na wani lokaci a ranar Lahadi. Wannan mataki ya biyo bayan matakin Jordan na kiran babban jakadanta a Bagadaza gida don tattaunawa bayan da masu zanga-zanga mabiya Shia suka dora tutar Iraqi a kan ginin ofishin jakadancin Jordan din.